Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa na daukar matakan da za su kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a kasar nan.
Tinubu ya fadi haka ne a wani jawabi bayan sanya hannu da wasu kamfanonin sarrafa nama na JBS a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil inda ake taron G20 masu karfin tattalin arziki a duniya.
Shugaban ya ce, rikicin manoma da makiyaya ya jima yana haifar da hasarar dukiya mai yawa a wasu yankunan Afirka, ba a Nijeriya kadai ba.
Kamfanin sarrafa nama na JBS ya amince da zuba jarin dala miliyan 2.5 domin gina kamfanonin sarrafa nama shida a faɗin Najeriya.
Kamfanin ya ce uku daga cikin kamfanonin za su mayar da hankali wajen sarar naman kaji, ayayin da biyu za su sarrafa jan nama, sai kuma guda wanda zai sarrafa nama aladu.