Gwamnatin Kano ta ce za ta hukunta duk wanda ta samu da yana amfani da babur mai kafa biyu domin sana’ar Achaba.
Mai bawa gwamnan Kano shawara kan harkokin Sufuri Alhaji Danladi Idris Karfi shi ne ya bayyana hakan, bayan samun rahotani kan yadda wasu ke ci gaba da gudanar sana’ar Acaba a birnin Kano, wadda tun a bayan gwamnatin jihar ta haramta.
“Gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ba za ta lamunci gudanar da sana’ar Acabar ba.
“Ci gaba da gudunar da sana’ar Acabar barazana ce ga harkokin tsaro a fadin jihar Kano”. In ji shi.
Mai Ba wa Gwamnan Shawara Ya kuma kara da cewa, duk wanda aka samu da laifin yin sana’ar Acabar zai fuskaci fushin hukumar nan take.
