Kungiyar Miyetti Allah ta kasa reshen Kudancin jihar Kaduna ta bayyana aniyar ta na haɗa kai da hukumomin tsaro, domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.
Hakan ya biyo bayan wani taron da aka gudanar a Kafanchan a ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar na yankin Kudancin jihar Kaduna, Alhaji Mato Yahaya ya ce, lokaci ya yi da za a samo mafita, tare da yin kira ga shugabanni su faɗi gaskiya kuma su gabatar da shawarwari masu amfani domin magance matsalolin rashin yankin.
Ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin makiyaya da sauran al’umma.
A nasa jawabin, shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jihar Kaduna, Alhaji Abdulhamid Albarka, ya ce an shirya taron ne domin tattara ra’ayoyin jagororin Fulani na kananan hukumomin jihar domin a mika su ga hukumomin tsaro dan ɗaukar matakin da ya dace.
