
Gwamnatin Kano na daukar matakai don inganta makarantun gwamnati, ta hanyar amfani da kudaden hayar kantunan kasuwanci da ke cikin harabar makarantu.
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB) ta tabbatar da hadin gwiwa da kananan hukumomi domin bunkasa ilimi da kula da makarantun gwamnati.
Shugaban SUBEB, Yusuf Kabir ne ya bayyana hakan yayin karbar rahoton kwamitin da aka kafa domin duba kantunan kasuwanci a harabar makarantun gwamnati.
Kwamitin wanda shugaban Karamar Hukumar Birni, Salim Hashim ya kafa, na da nufin ganin an tallafawa makarantun gwamnati domin magance matsalolinsu.

Shugaban ma’aikatan karamar hukumar Birni, Umar Aliyu Mustafa ya ce, an samar da tsare-tsare don amfani da kudaden hayar kantunan wajen kula da makarantu.
Daraktan wayar da kai na SUBEB, Balarabe Danlami Jazuli ya tabbatar da cewa za a sanya ido don hana karkatar da kudaden, domin tabbatar da amfani da su wajen bunkasa ilimi.