
Gwamnatin tarayya ta bayyana fara wani shiri na gwajin ƙasar noma domin tantance ingancin ƙasa da gano sabbin hanyoyi na inganta noma a Najeriya.
Matakin na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na tabbatar da wadataccen abinci da sauƙaƙa rayuwar manoma a fadin ƙasar.
Karamin Ministan Noma da Bunƙasa Samar da Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana haka hirarsa da Premier Radio a yayin wata ziyarar da ya kai tashar a yammacin ranar Talata.
Dakta Abdullahi, tsohon Sanata ne daga Jihar Neja, kuma kwararren likitan dabbobi, ya ce gwajin ƙasar noma zai bai wa manoma damar fahimtar irin takin da ya fi dacewa da gonakinsu, tare da rage asara da wahalhalun da suke fuskanta wajen noman amfanin gona.
“Wannan shirin na ɗaya daga cikin matakan da Ma’aikatar Noma ta ɗauka domin aiwatar da manufar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadataccen abinci ga al’umma.
“Manufarmu ita ce taimaka wa manoma su samu ingantacciyar ƙasa mai armashi, su kuma rage wahala, sannan su samar da abinci mai yawa cikin sauƙi,” in ji Ministan.
Ministan ya kuma ƙara da cewa Ma’aikatar Noma za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su inganta rayuwar manoma da bunkasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar harkar noma da kiwo.
Tattaunawar da aka yi da Ministan tsawon sa a guda a tashar ta shafi batutuwa masu muhimmanci da suka shafi noman zamani, kiwon lafiya, da kuma hanyoyin da gwamnati ke bi don sauƙaƙa rayuwar masu ruwa da tsaki a harkar noma.

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin ci gaba da wayar da kan manoma da samar da bayanai masu amfani domin tabbatar da dorewar abinci da bunƙasar tattalin arziki a ƙasar.