
Hukumar NiMET, ta yi hasashen samun ruwan sama da iska mai kafi a sassa daban-daban na kasar nan, daga ranar Litinin 22 zuwa Laraba 24 ga watan Satumba.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a Abuja a ranar Litinin ta ce, ana sa ran iskar tare da ruwan sama a jihohin Adamawa da Taraba da Kaduna da Kano da Gombe da Bauchi da Zamfara da Kebbi da Katsina da Sokoto da kuma Borno.
A yankin arewa ta tsakiya da ya haɗa da Abuja da Neja da Benue da Kogi da Filato da kuma Nasarawa. Sannan za a samu iska da hadari sanan daga bisani a iya samun ruwan sama mai karfi a wurare dabam-dabam. In ji hukumar.
A yankin Kudu kuwa ruwan sama da guguwa za a yi a jihohin Ebonyi da Abia da Imo da Enugu da Anambra da Legas da Ogun da Oyo da Ondo da Delta da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom dakuma Cross River.
Hukumar ta kuma yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohin Bayelsa da Ebonyi da Akwa Ibom da kuma Rivers, tana mai kira ga hukumomin agaji su dauki matakan kariya.
An kuma shawarci Direbobi da su yi taka-tsantsan yayin tuki a lokacin damina, haka nan ma manoma an gargade su kada su zuba taki ko feshi kafin ruwan sama domin kauce wa asarar sinadarai.
NiMet ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi sahihan bayanan yanayi a filayen jiragen sama kafin tsara tafiya.