
Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama tare da guguwa mai karfi a sassa daban-daban na ƙasar nan daga yau Litinin zuwa Laraba.
A cikin hasashen yanayi da ta fitar jiya Lahadi a Abuja, NiMet ta bayyana cewa za a sami guguwa mai ɗauke da matsakaicin ruwa da safiyar yau a wasu sassa na jihohin Kebbi, Zamfara, Sokoto, Gombe, Borno da Yobe a arewacin ƙasar.
Hukumar ta ce daga bisani da yammacin yau Litinin za a sami guguwa da iska a nan Kano da jihar Bauchi, Yobe, Jigawa, Kaduna, Zamfara, Katsina, Adamawa, Taraba da Borno.
A yankin arewa ta tsakiyar kuwa, ruwan sama za a samu a sassan jihar Plateau da Neja da safe, sai kuma iska tare da ruwan sama daga yamma zuwa dare a jihohin Nasarawa, Benue, Neja, Plateau, Kogi da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Hukumar ta roƙi jama’a da su ci gaba da bibiyar shafinta na yanar gizo domin samun ingantaccen bayani kan yanayi.