
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci zai yiwa ƙawanya a Najeriya zai ƙaru zuwa da kaso 3.6 cikin ɗari a shekarar 2027.
A wani rahoto da bankin ya fitar bayan ganawa tsakaninsa da asusun bada lamuni na IMF ya ce, dogaro da Najeriya ta yi kachokan kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa tattalin arzikinta ya ci gaba da rarrafe.
Bankin na duniya ya ce, har yanzu mahukuntan Najeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawa ba.
A cewar bankin, abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.
Bankin ya ce duk da ci gaban da Najeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawa.
Baya ga Najeriya, talakawan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo na cikin waɗanda za su ƙara fadawa cikin ƙangin talauci a 2027 in ji rahoton Bankin.