
Majalisar dokokin Kano ta amince da yin dokar kafa hukumar Kula da gudanar da dokokin ababan hawa ta jihar wadda aka dorawa alhakin kamawa, cin tara tare da gurfanar da masu Karya dokokin hanya a Kano.
Hakan ya biyo bayan amincewa da karatu na uku da majalisar ta yi akan dokar a zamanta na ranar Talata
Lawan Hussaini Dala, Shugaban masu rinjaye na majalisar ya ce, ayyukan da suka rataya a wuyan sabuwar hukumar sun hada da kama masu Karya kowacce irin dokar tuki a jihar.
Majalisar ta bada tabbacin cewa, da zarar Gwamna Abba Kabir Yusif ya sanya wa dokar hannu hukumar za ta fara gudanar da ayyukanta gadan-gadan domin tsaftace tuki a Kano da Kuma tarawa gwamnati kudin shiga.