
A karon farko tun bayan kafuwar rundunar sojin Najeriya ta nada mace a matsayin mai magana da yawun rundunar.
Wacce aka nada ita ce Laftanar Kanar Appolonia Anaele, ta kuma karbi muƙamin ne daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya kammala aikinsa a wannan matsayin.
Appolonia Anaele za ta fara aiki ne a hukumance daga ranar Talata mai zuwa, duk da cewa a halin yanzu tana matsayin mai riƙon muƙamin.
Wannan mataki na tarihi na nuna ci gaba wajen ƙara wa mata dama da wakilci a manyan muƙamai a cikin rundunar tsaro ta ƙasa.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙarfafa manufar daidaito tsakanin maza da mata a hukumomin gwamnati da na tsaro.