Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya sauya wa Mataimakinsa matsayi na kwamishina a Ma’aikatar Kananan Hukumomin jihar
Gwamnan ya sauya wa Kwamared Aminu Abdussalam matsayi na kwamishina a Ma’aikatar Kananan Hukumomi Ma’aikatar Ilimi na jihar zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar
Gwamman ya yi wannan sauyin ne a cikin jerin sauye-sauye da ya yi a Majalisar Zartarwas jihar a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da Kakakin gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce, Mataimakin Gwamnan ya canji Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, wanda aka canza daga ma’aikatar zuwa Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Kirkire-Kirkire.
Yayin da Honorabul Mohammad Tajo Usman, dake wurin aka mayar da shi Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Al’adu.
Sauran wadanda sauyin ya shafa sune Honorabul Amina Abdullahi da aka dauke daga Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci zuwa Ma’aikatar Mata da Yara da Nakasassu. Sai Honorabul Nasiru Sule Garo daga Ma’aikatar Muhalli da Canjin Yanayi zuwa Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
Kwamishinan Kula da Ayyukan Duba da Kimantawa Honorabul Ibrahim Namadi, yanzu ya koma Ma’aikatar Sufuri. Yayin da Honorabul Umar Haruna Doguwa na Ma’aikatar Ilimi yanzu ya koma Ma’aikatar Ruwa.
Sauran wadanda aka canza mukamansu sune Honorabul Ali Haruna Makoda daga Ma’aikatar Ruwa zuwa Ma’aikatar Ilimi. Sai Honorabul Aisha Lawal Saji daga Ma’aikatar Mata Yara da Nakasassu zuwa Ma’aikatar Harkokin Yawon Shakatawa da Al’adu, da Honorabul Muhammad Diggol daga Ma’aikatar Sufuri zuwa Ma’aikatar Duba Ayyuka da Kimantawa.
A wannan sauye-sauyen Gwamna Yusuf ya cire Kwamishinoni guda biyar; Ibrahim Jibril Fagge na Ma’aikatar Kudi da Ladidi Ibrahim Garko ta Al’adu da Yawon Shakatawa.
Da Baba Halilu Dantiye na Harkokin Watsa Labarai da Harkokin Cikin Gida. Shehu Aliyu Yammedi na Ayyuka na Musamman. Da kuma Abbas Sani Abbas na Ci Gaban Karkara da Al’umma.
Gwamnan ya umurci Shugaban Ma’aikata da Kwamishinoni guda biyar da aka cire da su tafi ofishin Gwamna domin yiwuwar sake musu mukamai da wuraren aiki.