Ƙungiyoyin agaji na duniya sun bayyana damuwa game da yawan yunwa da ke ta’azzara a arewacin Najeriya, wadda suka alaƙanta da raguwar kuɗaɗen tallafi daga ƙasashen waje.
Ƙungiyar likitoci ta Medecins sans Frontieres ta ce yara 600 ne suka mutu waɗanda take kula da su a sansanoninta cikin wata shida da suka wuce saboda ƙarancin abinci mai gina jiki.
Ita kuwa kungiyar World Food Programme ta ce za ta dakatar da bayar da duk wani agajin yaki da yunwa a arewa maso gabashin Najeriya cikin wata mai zuwa saboda ƙarancin kuɗi.
Yawan kuɗin da aka daina bayarwa, wanda gwamnatin Amurka karƙashin Donald Trump ta fara yi, ya haɗu da hauhawar farashi da kuma hare-haren ta’addanci domin ta’azzara lamarin.
