Wani jirgin saman sojan Sudan ya yi hatsari a yankin Omdurman da yammacin Talata, inda fasinjoji da sojoji da dama suka mutu, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Suna.
Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce, jirgin ya faɗo ne yayin da yake yunƙurin tashi daga filin jirgin sama na Wadi Seidna.
Jaridar Sudan Tribune da ke birnin Paris ta ruwaito cewa, fararen hula aƙalla biyar ne suka mutu sannan da yawa suka ji rauni lokacin da ɓaraguzai suka rikito a kusa da gidajen jama’a.
Ta kuma ambato wasu majiyoyin soji da suka ce lamarin ya faru ne sakamakon matsalar na’ura, kuma akwai manyan jami’ai a cikin fasinjojin.
