
Shugaban kamfanin Mai na kasa NNPCl Mista Bayo Ojulari ya ce, nan gaba kadan za cigaba da aikin tono mai a arewa.
Kimanin shekara biyu bayan ƙaddamar da aiki haƙo ɗanyen man fetur a kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe – wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba – a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin.
Aikin da aka ƙaddamar a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘ƴan Najeriya ke ci gaba da koka wa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.
Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ya sanar da cire tallafin man fetur