Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga gadin manyan mutane domin mayar da su kan aikin tsaro.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne yayin ganawar sa da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar a ranar Lahadi a cewar Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga a wata sanarwa da ya rabawa menama labarai.
Shugaban kasa ya bayar da wannan umarnin ne yayin ganawar sa da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan a fadar shugaban kasar dake birnin tarayyar Abuja ciki har da babban Sufeto na yan sanda Kayode Egbetokun.
“Gwamnati ta lura da yadda yankunan karkara suke fama da karancin jami’an yan sandan, wanda kuma haka ya kara ta’azzara rashin tsaron da hakan ya bawa yan ta’adda damar gudunar da aiyukan su.ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin ne domin sake tabbatar da tsaro a fadin kasar.” In ji sanarwar
Shugaba Tinubu ya kuma ce, Daga yanzu duk mutumin da ke son jami’an tsaro su yi gadinsa, sai dai ya nemi jami’an hukumar tsaron ta Civil Defence.
