Wakilai daga Amurka da Ukraine da ƙasashen Faransa da Birtaniya da kuma Jamus ake sa ran za su yi wata tattaunawa a Geneva kan daftarin shirin gwamnatin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine
Shugaba Trump ya ba wa Ukraine wa’adin ranar 27 ga watan Nuwamba domin amincewa da shirin kawo ƙarshen yaƙin da aka kwashe kusan shekaru hudu ana gwabzawa.
Sai dai gwamnatin Kyiv na buƙatar a yi sauye-sauye ga daftarin kafin ta amince da wasu daga cikin buƙatun na Rasha kan kawo karshen yakin.
Shugabannin Turai sun yi amannar cewa wannan zaman, da alama an kama hanyar kawo ƙarshen yaƙin Rasha, sai dai duk da haka akwai jan aiki a gabansu.
