
Yau ake bukuwan Sallah da aka saba yi bayan ganin watan Shawwal da ya kawo karshen azumin watan Ramadan.
A nan Najeriya an tashi da Bikin ne a sakamakon sanarwar ganin jinjirin wata da Sarkin Musulmi yayi a daren Asabar.
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi shi ma ya sanar da ganin watan wanda ya kawo karshen azumin na wannam shekarar.
Sai dai ba kamar yadda aka saba ba, a wannan sallar babu hawan Sallah na al’ada da aka saba yi a lokacin Bikin a kowacce shekara.
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi shi ma ya sanar da dakatar da hawan bayan da Jami’an tsaro suka sanar da hana hawan a bisa dalilai na tsaro.
Tuni Gwamnatin tarayya ta bayar da ranakun Litinin da kuma Talata hutun don bukuwan Sallah.