Yau Shekara 10 da tashin Bam a babban masallacin Juma’a na Kano ana tsaka da sallah
A rana mai kamar ta yau 28 ga watan Nuwambar shekarar 2014 ‘yan Boko Haram suka tashi bama-bamai a na tsaka da sallar Juma’a tare da harbin kan-mai-uwa-da-wabi.
Wannan na cikin muggan hare-haren ta’addanci da aka gani a tsawon shekarun da Boko Haram tana yi a arewacin kasar nan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daruruwan mutane ne aka kashe a harin, ana kuma hasashen adadin ya fi haka.
Sakamakon harin, rayuwar mutanen jihar ta sauya domin hukumomi sun ɓullo da matakai daban-daban domin katse hanzarin maharan.
A lokacin an taƙaita zirga-zirga da hana fitar dare da datse hanyoyi da kafa shingayen binciken da kuma caje masu shiga wuraren ibada da sauransu.