Premier Radio ta cika Shekara 3 da kafuwa
A yau 11 ga watan Disamba shekarar 2021 Premier Radio ke cika shekaru uku da fara gabatar da shirye shirye a birnin Kano.
Tashar ta zo da sabon salo na labarai a duk sa’a, wanda kuma masu sauraron tashar ke bayyana cewa salon ya zo a gabar da ake tsaka da bukatarsa.
Hakan kuma ya yi tasiri wajen bunkasar tashar a kunnuwan masu sauraro
Yana daga cikin abubuwan da tashar ta banbanta da shi wato ma’aikata, inda tashar ta samu zakakuran matasa da suka zama masu jan ragamarta zuwa inda take a yanzu da kokarin kaita fiye da inda take a shekarun gaba masu zuwa.
A bangaren shirye shirye ma tashar ba a barta a baya ba, domin tana da shiri na musamman kan mata, matasa, addini, wasanni, lafiya, siyasa da sauransu.
Kazalika tashar ta kuma kara yin zarra tsakanin takwarorinta wajen samar da wani shiri na musamman mai suna Grassroot wanda yake iske alumma har inda suke don tattaunawa da su kai tsaye kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu kai tsaye.
Akwai tarin nasarori dama kalubale da tashar ko kuma ma’aikatan ta suka fuskanta a wadannan shekaru da idan kun biyo mu a shirye shiryen mu na musamman da muka tanadar muku zaku ji karin bayani a cikin shirye-shirye na musamman da za a gabatar.
Ga wasu ma’aikatan Gidan radiyon a bakin aiki