A ranar Laraba da ake bikin Krisimeti, shugaban jam’iyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano ya cika shekara 75 da haihuwa.
An haifi tsohon gwamnan ne a ranar 25 ga watan Disambar shekarar 1949 a garin Ganduje dake Dawakin Tofa a jihar Kano.
Bayan karatun Allo da na Islamiya, ya shiga makarantar Firamare ta Dawakin Tofa a shekarar 1956 zuwa 1963.
Ya kuma ci gaba da karatunsa a Kwalejin Horas da Malamai ta Birnin Kudu da kuma Kwalejin Ilimin Mai zurfi ta Horas da Malamai Ta Kano, a tsakanin shekarun 1964 zuwa 1972.
Ganduje ya yi karatun digirinsa na farko a Jami’ar Bayero, na biyu kuma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria sai na uku a Jami’ar Ibadan a tsakanin shekarun 1984 zuwa 1993.
Tsohon gwamnan ya tsunduma harkar siyasa a shekarar 1979 da shiga jam’iyyyar NPN a inda ya tsaya takarar Majalisar Wakilai amma bai yi nasara ba.
Bayan aikin gwamnati tare da rike mukamai daban daban a Hukumar FCDA a shekarun 1984 zuwa 1994, ya zama kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano a karkashin mulkin soja.
Da aka soma siyasa ya shiga jam’iyyar PDP a 1998, ya kuma yi wa Rabiu Musa Kwankwaso mataimakin gwamna a mulkinsa na farko da na biyu.
Ya kuma karbi ragamar mulkin jihar a 2015 ya kuma yi shekara takwas
Abdullahi Ganduje ya zama shugaban jami’iyyar APC mai mulki ne a ranar 3 ga watan Agustan 2023