An kammala kada kuri’u a wasu daga cikin rumfunan zabe da ke jihar rivers, ana cigaba da kirga kuri’u.
A yau Asabar ne mutanen jihar Rivers suka fito domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar guda 23.
Jihar na da akwatunan zaɓe guda 6,866 a mazaɓu 319, inda za a gudanar da zaɓe domin maye gurbin shugabannin da kotun ƙolin kasa ta sauke.
Kimanin wata shida da suka gabata ne kotun ƙoli ta yanke hukuncin soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka yi a ranar 5a ga watan Oktoban shekarar 2024, wanda hukumar zaɓen jihar ta shirya.
A wancan lokacin zaɓen ya ɗauki hankali ne kasancewar Ministan Abuja, kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya ja daga da dakataccen gwamnan jihar, Sim Fubara, wanda a
