
Biyo bayan sakin wasu mata 3 da Hamas ta yi cikin aikin da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakaninsu da ya soma aiki
Ta sako Falasdinawan ne wayewar garin Litinin a cikin wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla wanda ya soma aiki safiyar Lahadi
Hukumar kula da gidajen yarin Isra’ila ta ce ta kammala sakin Falasɗinawa fursunoni 90, a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta soma aiki ranar Lahadi.
“An saki dukkan fursunoni daga gidan yarin Ofer da kurkukun Birnin Ƙudus”, in ji wata sanarwa da hukumar ta fitar kafin ƙarfe 1:30 na dare.
TRT ta rawaito cewa, wata babbar motar ɗaukar kaya, ɗauke da gomman fursunonin, dukkansu mata da ƙananan yara, ta fita daga kurkukun Ofer da ke wajen birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Sannan dukkan waɗanda aka saka mata da ƙananan yara ne, a cewar wani jadawali a Hukumar Kula da Harkokin Gudanarwar Falasɗinawa.
An gudanar da bukukuwan sako da fursunonin a birnin na Gaza wacce Isra’ila ta yiwa raga-raga.
Isra’ila ta saki Falasɗinawa fursunoni 90