
Rundunar yansanda ta kafa wani kwamitin mutum takwas domin bincikar rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da na Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Kwamishinan ‘Yansandan jihar, Ibrahim Bakori ne ya sanar da haka a daren Laraba yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin kungiyar wakilan kafafen yada ta kasa reshen Kano waɗanda suka kai masa ziyara.
“Kwamitin na da aikin gano musabbabin rikicin domin gano waɗanda ke da hannu da kuma ba da shawarwari kan matakan da ya kamata a ɗauka.” In ji shi.
Kwamishinan ya kuma ce, an kaddamar da kwamitin ne a ranar Litinin, kuma ana sa ran zai mika rahotonsa cikin kwana bakwai.

Rikicin dai ya faru ne a ranar Lahadi a fadar Kofar Kudu, lokacin da sarki Aminu ke komawa fadar Nassarawa bayan ziyarar ta’aziyya da ya kaiwa iyalan marigayi, Alhaji Aminu Alhassan Dantata a unguwar Koki, kan hanyarsa ta dawowa ya biyo ta fadar sarkin a Kofar Kudu.
A wata sanarwar da Fadar Sarki Sanusi ta fitar, wadda ta samu sa hannun Saddam Yakasai, ɗaya daga cikin jam’ian yaɗa labarai na fadar, ta zargi Sarki Aminu Ado da hannu a harin da aka kai Gidan Rumfa.
” ‘Yan daban Aminu Ado ne suka kutsa cikin Gidan Rumfa bayan ɓalla ƙofa, suka kai wa masu tsaron gidan hari tare da jikkata wasu, sannan suka lalata abubuwa da dama ciki har da motocin jami’an tsaro da ke ajiye a fadar.
“Da gangan Sarki Aminu ya bi ta wannan hanyar domin mutanensa su kai hari a fadar lokacin da yake komawa gida bayan yi wa iyalan Aminu Alhassan Dantata ta’aziya.” In ji Sanarwar.
Ɓangaren Sarki Sanusi ya kuma ce ba wannan ne karon farko da Aminu Ado ke bin hanyar ba, “a baya ma ya taɓa bin hanyar domin ya razana mutanen unguwar”.
Makusancin Aminu Ado Bayero wato Aminu Babba Dan Agundi ya ce tabbas ba wannan ne karon farko da tawagar Aminun ke bi ta hanyar Gidan Rumfa ba – Fadar Sarki Sanusi – “sai dai babu wani abu da ya taɓa faruwa”.
Aminu Dan Agundi ya kuma ce, “mun je ta’aziya gidan Alhaji Aminu Dantata, muka biyo ta cikin gari, za mu wuce ta ƙofar gidan sarki na gidan Rumfa, sun saka ƴan daba, muna wucewa suka fara jifa suka yo kan mutane.
“Mutanenmu da suka ga haka sai suka kora su, kuma akwai bidiyo, kowa zai iya gani,” in ji Dan Agundi.
Aminu Babba Dan Agundi ya kuma zargi fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ƙoƙarin shafa masu kashin kaji ta hanyar zargin su da kai harin.
Rahotanni sun ce rikicin ya haifar da raunuka ga wasu daga cikin masu tsaron fadar da rushe daya daga cikin ƙofofin shiga fadar da kuma lalata wasu motocin ‘Yansanda da ke wajen.
Daga bisani, rundunar yansanda ta tabbatar da kama mutane hudu da ake zargi da hannu a cikin rikicin.