
‘Yansanda a jihar Neja sun kama wasu mutane su 9 a bisa zargin aikata laifin garkuwa da kansu don neman kudin fansa.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ne ya bayana haka a hirarsa da manema labarai a jihar a ranar Laraba.
Ya na mai cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Satumbar 2025, a lokacin da aka samu rahoton garkuwa da wani mutum a unguwar Mandela da ke Minna.
“Daga baya kuma aka samu kira daga wata lamba, tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan Bakwai a ranar 3 ga watan Satumba.
Hakan ta sa ’Yansandan suka kama wani mutum mai suna Suleiman Dauda. Bayan yi masa tambayoyi, an kuma kama wasu mutane takwas a unguwar Mandela”. In ji shi.
Kakakin ya kuam kara da cewa, a lokacin gudanar da bincike an samu layin waya guda 21 da takardun rijistar layi guda 29 a wajen Suleiman, wanda ya ce yana harkar rijistar layin ne.
Wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya bai wa waɗanda “aka sace” waya da lambar da aka yi amfani da ita wajen neman kuɗin fansa.
