
Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ta janye Kiran da ta yi wa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II zuwa Abuja.
A cikin sanarwar da Rundunar ta fitar mai sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi a yammacin Lahadi ta ce, hakan biyo bayan shawarar da masu ruwa da tsaki suka bayar ne.
Da kuma gudun kar a yi wa aikin rundnar mummunar fahimta ko kuma siyasantar da gayyatar.
Maimakon zuwa Abuja Baban Sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun ya umarci ƴan sashen tattara bayanan sirri da su je jihar Kano domin karbar bayanan Sarkin dangane da abin da ya faru a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama.