
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake haramta duk wani nau’i na hawan Sallah a yayin bukukuwan Babbar Sallar da ke tafe.
Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata.
Ya kuma ce, haramcin da rundunar ta fitar na hana hawan sallah karama na nan daram kuma za su tabbatar da an yi aiki da ita a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta 2025.
“Daga cikin dokokin shi ne su kaurace wa hawa doki ko ma kowacce irin dabba da sunan kilisa ko tseren mota ko tukin ganganci ko rike makami.
“Kazalika, an haramta amfani da makami ko kuma duk wani abu da zai iya razanar da jama’a, yayin da ake kiran al’umma da su ja kunnen ’ya’yansu su kauce wa karya doka.
“’Yan sanda suna ba mutane shawara da su bi dukkan dokokin da aka kafa a lokacin bukukuwan.
“’Yan sanda da suran jami’an tsaro a shirye suke su tabbatar da an bi wannan doka tare da hukunta wadanda suka karya ta,” in ji sanarwar.
Kakakin ya kuma ce, sun dauki matakin ne bayan wani zama da ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi, a inda suka gano wani yunkuyi da aka yi wajen yin amfani da hawan domin yi wa harkokin tsaron jihar zagon kasa, kamar yadda aka samu yayin Karamar Sallar da ta gabata.
Kafin sanarwar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya umarci Hakimai da su shigo birnin Kano domin fara shirye-shiryen hawan na Babbar Sallah da za yi a ranar Juma’a.
Umarnin Sarkin na kunshe ne a cikin wata wasika da masarautar ta aike wa Hakiman jihar, a inda ta bukaci da su taho tare da dawakai da mahayansu.
Wasikar dai na dauke da sa hannun Sakataren masarautar kuma Dan Makwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf dauke da kwanan watan 30 ga watan Mayun 2025.
Idan za a iya tunawa, ko da Karamar Sallar da ta gabata, Sarkin na Kano ya gudanar da hawan duk kuwa da sanarwar ’yan sandan ta hana shi, lamarin da ya sa hedkwatarsu ta kasa ta gayyace shi, kafin daga bisani ta janye gayyatar bayan abin da ta kira sanya bakin wasu masu fada a ji.