Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da satar motoci tare da kwato motoci uku.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta kama Aliyu Mamman mai shekaru 35 a unguwar Hotoro, da Abdulhamid Usman da Saliha Abdulhamid da Auwal Shuaibu da Sani Bala da kuma Ahmad Mannir, inda aka kwato motocin a wajan su.
Sanarwar ta jaddada cewa rundunar na ci gaba da bincike tare da kira ga al’umma su rika bayar da bayanai kan duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
