’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal, sun kuma yi garkuwa da dalibai 25.
Lamarin ya faru ne a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati a yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.
Wani mazaunin Maga, Aliyu Yakubu ya ce, maharan sun shigo makarantar ne kimanin ƙarfe 5 na safiyar Litinin.
“ ‘Yan taddan sun harbe Shugaban Makarantar ne a lokacin da yake ƙoƙarin kare ɗalibansa daga faɗawa hannun ƴan bindigar.
“Rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga makarantar da kuma al’ummar yankin gaba ɗaya”. In ji shi
Harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali, abin da ya sa jama’a ke cikin tsananin damuwa da alhini.
