
’Yan Sandan sun samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar 7 ga watan Oktoba.
Ya ce runduna ta musamman ta yaƙi da garkuwa da mutane tare da haɗin gwiwar tawagar sintiri ta sashen ’yan sanda na Bebeji suka kai samame, bayan samun bayanan sirri.
An ceto mutanen ne, bayan wani matashi mai shekaru 21, mai suna AbdulHamid Bello, wanda aka sace, ya yi nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da shi, ya sanar da ’yan sanda inda aka ajiye shi.
Wannan ya taimaka wajen gani maɓoyar masu garkuwar da ke ƙauyen Saya-Saya, a Ƙaramar Hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka samu nasarar ceto wani mutum mai suna Musa Idris, mai shekaru 65.
Masu garkuwar sun tsere bayan ganin ’yan sanda, inda suka bar babur da igiya.
Daga baya, an mayar da waɗanda aka ceto zuwa ga iyalansu tare da kai su asibiti don kula da su.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya umurci a kula da lafiyar waɗanda aka ceto, tare da tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da neman waɗanda suka tsere.