Rundunar ‘yan sandar jihar Kano sun kama kudin jabu na miliyoyin Naira
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutum uku da ake zargi da mallakar kudin jabu da suka kai sama da Naira miliyan dubu dari da ashirin da tara da aka shigo da su nan Kano domin damfarar al’umma.
Kakakin ‘yansandan Kano, Safritanda Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana haka lokacin da ya aka yi holin mutanen, da ma sauran wadanda aka kama da laifuka daban-daban.
Daya daga cikin wadanda ake zargi ya ce, sun shigo da kudin ne daga jihar Legas da niyyar shigar da su cikin kasuwancin jihar.