
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu nasarar ceto wani tsoho mai shekaru 75 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Tsohon mai suna Abdulrahman Yunusa, mazaunin Maigana a Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, ya kubuta ne bayan da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace shi.
A sanarwar da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a daren Lahadi, ta bayyana cewa bayan samun sahihan bayanan sirri, rundunar ta kai samame a wani kauye mai suna Bagau da ke karamar hukumar Bebeji a Kano, inda aka gano maboyar masu garkuwa da mutanen.
An gudanar da samamen ne a ranar 9 ga Mayu, 2025 a inda rundunar ta kama wani matashi mai suna Musa Tukur dan shekara 23 daga Karamar Hukumar Kudan ta jihar Kaduna. An same shi yana tsare da tsohon, wanda aka daure masa hannaye da igiya tare da rufe masa idanu da zane.
Wanda ake zargi ya amsa cewa shi da wasu abokan aikinsa ne suka sace Abdulrahman daga gidansa a ranar 3 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 12:30 na rana. Sun kuma nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan ashirin (₦20,000,000).
Bayan ceto tsohon, an garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa, kafin daga bisani a mayar da shi hannun iyalansa a jihar Kaduna.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da samamen bisa jajircewa da kwarewarsu, tare da godewa al’umma bisa gudummawar bayanai masu amfani da suka bayar wajen yaki da laifuka a jihar