‘
Yan bindiga sun sako Sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya, Hamza Musa Durba, bayan sace shi da akayi a daren Juma’a 20 ga Maris 2026 a Jihar Kano.
wannan na cikin sanarwar da hadimin dan majalisar Kano mai wakiltar karamar hukumar Kibiya, Musa Shehu Autan Fammar ya fitar.
Sanarwar tace sakataren mulkin ya shaki iskar yanci ne bayan shafe kwanaki 4 a hannun masu garkuwa.
