Wasu ’yan bindiga akan babura sun kai hari cikin garin ‘Yan Cibi Tsohon Gari a karamar hukumar Tsanyawa sun kuma sace shanu sama da 60.
Lamarin ya faru ne a daren Asabar.
Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa, jama’a da dama sun tsere daga gidajensu saboda tsoro.
‘Yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mata, amma daga baya sun sake su bayan sojoji sun isa wurin domin kai agaji.
Wasu daga cikin mazauna garin ya ce, sun fara shirin barin garin gaba daya saboda tsananin hare-haren.
Garin Yan Cibi na kan iyakar jihar Kano da jihar Katsina, yana daga cikin yankunan da aka fi samun hare-haren ’yan bindiga a jihar Kano.
