Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kira ga Saudiyya da ‘sauran yan kungiyar OPEC su rage farashin mai a Duniya.
Trump ya bayyana haka ne a taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Davos.
Sabon shugaban na Amurka ya yi barazanar ƙara haraji kan man fetur idan ba su yi hakan ba.
Ya kuma ce, ya yi mamakin yadda ƙungiyar OPEC ta kasa rage farashin man tun kafin ya hau mulki.
Jawabin nasa ya zo ne kwana guda bayan zantawarsa ta waya da Yariman Saudiyya, Muhamad bin Salman.
A cewar, rahotanni daga kafofin yada labaran Saudiyya, Yarima bin Salman ya alƙawarta zuba jarin dala biliyan 600 a Amurka cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Sai dai, sanarwar da fadar White House ta fitar bayan ganawar shugabannin biyu ba ta ambaci waɗannan adadin ba.