Ƙungiyar likitoci ta duniya MSF ta ce mutanen da take bai wa kulawa a sansanin raba kayan agajin da Amurka ke goyon-baya a Gaza sun ba da labarin yadda sojojin Isra’ila ke yi musu ruwan wuta.
Sun ce ana harbin su ta kowanne ɓangare kama daga jirage marasa matuka da helikwafta,da jiragen ruwa, da tankokin yaƙi.
Wakiliyar BBC ta ce bayanan da ƙungiyar MSF ta fitar sun ci karo da wadanda Isra’ila ke bayarwa cewa ba ta harbi kan fararen hula da ke zuwa karbar abinci a Gaza.
Wani mutum da MSF ta tattauna da shi ya bayar da labarin yadda ake cewa su zo su karbi abinci, amma sai a ɓuge da harbi kan mai tsautsayi.
Ƙungiyar ta ce wannan salon raba tallafin na tattare da mugun haɗari da cutarwa.
