Mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam ya karbi aiki daga hannun Kwamishinan Ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata.
Yayin da tsohon Kwamshinan Ilimi Mai Zurfi ya karbi aiki a hannun na Muhammad Tajo Othman a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da kuma Kere-Kere duk a ranar Litinin kamar yadda gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarni.
Ga yadda Kwamishinonin biyu suka kama aiki a sabbin ma’aikatun nasu cikin hotuna
Mataimakin Gwamna kuma sabon Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi yayin karbar ragamar Ma’aikatar daga Dakta Yusuf KofarMata mai barin gadoKwamishina Yusuf na yi wa ma’aikatan Ma’aikatar jawabi a yayin bikin sauyin ragamar mulki Sabon Kwamishinan da Kwamishina mai barin gado da kuma sauran ma’aikatan a yayin bikin karbar ragamar mulkinKwamishina Yusuf Kofar Mata da ‘yan rakiya a sabuwar Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da kuma Kere-kere yayin isarsa ma’aikatar Sabo Kwamishinan Ma’aikatar Yusuf Kofarmata da Tsohon Kwamishina Muhammad Tajo Othman suna tattauna wa Kwamishina Muhammad Tajo Othman yayin mika mulki ga Yusuf Kofar Mata a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da kuma kere-kere Sabon Kwamishinan yana hira da ‘yan jaridu bayan kammala bikin mika ragamar mulki a ma’aikatar