
Kwalejin Koyar da Ilimin Addini da Shari’ar Musulunci ta Aminu Kano, (AKCILS) ta bayyana shirinta na fadada tsarin karatu domin fara bayar da shaidar digiri a fannoni daban-daban.
Kwalejin da aka fi sani da Makarantar LEGAL, za ta yi hakan ne cikin hadin gwiwa da manyan jami’o’in gwamnatin tarayya.
Shugaban kwalejin, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada ne ya bayyana hakan yayin rantsar da sabbin dalibai na zangon karatu na 2024 zuwa 2025 a dakin taro da ke cikin makarantar.
A cewar Farfesa Jakada, adadin sabbin daliban da suka samu gurbin karatu a bana ya kai 3,341, inda 2,430 daga cikinsu za su yi karatun NCE, yayin da 911 za su karanci Diploma a fannoni daban-daban.
Za kuma ta cigaba da bayar da shaidar Diploma matakin kasa a bangarorin ilimi da dama.
Farfesa Jakada ya bukaci sabbin daliban da su kasance masu bin doka da oda, tare da kiyaye dokokin makarantar, domin gujewa fadawa cikin halayen da ka iya janyo musu hukunci ko ladabtarwa.
A jawabinsa a wajen taron, Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, wanda kuma shi ne Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da goyon bayan kwalejin domin tabbatar da cewa tana samar da ilimi mai inganci da nagarta.
Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Darakta mai kula da tsare-tsaren karatu na ma’aikatar, Malam Musa Gambo Sharifai, ya jaddada cewa gwamnati tana daukar ilimi a matsayin ginshikin ci gaban al’umma, don haka ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tallafa wa kwalejin LEGAL da sauran cibiyoyin ilimi ba.