Babban lauya mai mukamin SAN ya kuma ce, mutane na yaudarar kansu ne kan wannan batu da yake karara a doka
Fitaccen lauya mai kare hakkin bil Adama, Femi Falana SAN ya ce, la’akari da hukuncin Kotun Daukaka kara, Sarki Sunusi shine tabbataccen sarkin Kano.
Falana wanda ya fadi hakan ne a cikin wani hoton bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta a makon nan.
A cikin bidiyo, Falana ya bayyana Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi na II a matsayin halastaccen sarki kuma zama daram duk da tababar da ake yi dangane da rikicin Masarautar Kano.
“Dole ne mu fada wa kanmu gaskiya a matsayinmu na lauyoyi. Saboda haka ina taya Mai Martaba murna dangane da nasarar da ya samu a Kotun Daukaka Kara.
“Duk da cewa masu adawa da kai [Sarki Sanusi] sun ce za su garzaya Kotun Koli, dole ne kuma mu a matsayinmu na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) mu yi ruwa da tsaki a lamarin.
“Dole ne a fahimci tanadin da doka ta yi dangane da hurumin kowacce kotu dangane da mas’alar da ta shafi masarauta.
“Abu na biyu kuma shi ne Kotun Tarayya ba ta hurumi kan abin da ya shafi masarauta, saboda haka idan ma har akwai wasu lauyoyi da ke ganin Kotun Koli na abin fada a wannan lamari to kuwa suna yaudarar wadanda suke wakilta.
“Ire-iren wadannan lauyoyi suna kawo matsala a kasar nan kuma nauyi ya rataya a wuyan Kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta shiga ta yi ruwa da tsaki domin a yi wa tufkar hanci.
“Mai Martaba [Sarki Sanusi] ya sani cewa duk ma inda waɗannan lauyoyi za su je, kana nan zama daram a kujerar mulki kuma dole Sarki daya tilo ne a Kano.
“Ba zai yiwu a ce akwai sarakuna biyu ba ne a Kano ko Shugaban Majalisar Dokoki biyu a Ribas. Dole ne a kawo karshen wannan rudani.”
Ana iya tuna cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron karar da ta shafi soke masarautun Jihar Kano.
Kotun a hukuncinta na farko ta ce Babbar Kotun Kano ce kawai take da damar yanke hukunci kan duk wani rudani da ya shafi sarauta a jihar.
Sai dai an samu sabani tsakanin alkalai uku da suka yanke hukunci kan lamarin.
Mai shari’a Gabriel Kolawale, wanda shi ne ya karanto hukuncin ya umarci da a mayar da karar zuwa kotun da ta dace, wato Babbar kotun Kano domin ci gaba da sauraro.
Sai dai sauran alkalan biyu sun ki amincewa da batun mayar da karar zuwa Babbar kotun jihar Kano, inda suka bayar da umarnin watsi da batun shari’ar baki dayanta.
A hukunci na biyu kuma kotun daukaka kara ta yi watsi da matakin Babbar kotun Kano na haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu na jihar bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha ta bayyana cewa akwai kuskure a hukuncin Babbar kotun Kano na ranar 15 ga watan Yulin 2024, kuma ya saɓa wa ka’idar jin ta-bakin kowane bangare.
Kotun ta kuma umarci alkalin kotun ta Kano ya miƙa shari’ar ga wani alƙalin na daban domin a sake sauraron shi daga farko.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukuncin kotun ta Kano na cike da “rashin adalci da saɓa ƙa’idar bai wa kowane ɓangare dama.”
Kotun ta ce Babbar kotun Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar ne ba tare sanar da Aminu Ado Bayero game da ƙarar ba, kuma ba a ba shi damar gabatar da nasa hujjojin ba.
Rikicin Masarautar Kano
Rikicin masarautar Kano na baya-bayan nan ya samo asali ne daga matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka a 2023, inda gyaran da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar ta bai wa gwamnan jihar damar rushe masarautu biyar na jihar.
Wannan ne ya bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf damar sauke Aminu Ado Bayero da sarakunan masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano daga kan muƙamansu. In ji jaridar Aminiya