Kungiyar Tuntuba Ta Arewa (ACF) ta ce, akwai bukatar sauya salon yadda ake yaki da ta’addaci musamman a Arewacin kasar nan.
Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Dalhatu shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da BBC
Dattijon ya bayyana damuwarsa kan yadda lamuran tsaro ke kara taɓarɓarewa a yankin Arewa.
“Dawo da tsaffin jami’an tsaro wadanda suka yi ritaya bakin aiki, zai taimakwa wajan yaki da ta’addacin baki dayan sa. In ji shi.
Shugaban kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan, ya kuma bayyana wasu daga cikin ayyukan da kungiyar ta gabatar a tsahon shekaru 25 da kafata.
Ya kuma nuna damuwar sa yadda ake ci gaba da samun karuwar yaran da basu zuwa makaranta, wanda a cewar hakan hakan barazanar tsaro ce.
Alhaji Bashir Dalhatu ya tabbatar da cewa, burin kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan a yanzu haka shi ne koyar da matasa maza da mata sana’oin da zasu dogara da kan su.
