10 daga cikin limaman Juma’a za su je Misira karo ilimi daga kananan hukumomin Gaya da Ajingi da kuma Albasu
Jami’ar Al-Azhar dake birnin Al-Kahira ta Misara sune suka turo Malaman su don yi wa Limaman bitar a masarautar Gaya.
Mai martaba Sarkin Gaya Alh. Aliyu Ibrahim ne ya dauki nauyin bitar, karkashin jagorancin Sarkin Malaman Gaya Malam Munzir Dakta Yusuf Ali.
Bayan kammala bitar ta kwana biyu, an yiwa limaman jarrabawa, an kuma zabi goman farko wanda suka fi maki. Wadanda Jami’ar za ta dauki nauyin karatunsu na wata uku a Misira
Taron kammal bitar ya samu halatar Maimartaba Sarkin Gaya, Wanda Maigirma Wamban Gaya Alhaji Mansur Ibrahim Abdulkadir ya wakilta da Kwamishina kula da harkokin addini Sheikh Ahmad Sani Auwal.
Sauran sune Mai taimakawa Gwamna na musamman Akan Harkokin Addini, da Kuma Shugaban Majalisar Malamai Ta arewa Maso Yamma Sheikh Malam Ibrahim da kuma Sauran Manyan Hakiman Masarautar Gaya.