Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC).
An yi bikin rantsuwar ne a ɗakin taro na Majalisar Ministoci dake Fadar shugaban ƙasa a Abuja, a ranar Laraba.
A jawabin shugaba Tinubu ga sabon shugaban hukumar, ya umarace shi da ya yi aiki “bisa gaskiya”.
A ranar 16 ga watan Oktoba ne majalisar dokoki ta amince da naɗa Farfesa Amupitan a matsayin shugaban hukumar (INEC).
Tinubu ya kuma ce, ya miƙa sunan Amupitan ne da kuma amincewar da majalisa ta yi hujja ce ta ƙwarewarsa da kuma yardar da aka yi da majalisar ministoci da ta dokoki suka yi da kai.
Tinubu ya kuma kara da cewa, ɗaya daga cikin ƙalubalen da ke gaban sabon shugaban shi ne gudanar da babban zaɓe na 2027 wanda kowane ɓangare zai amince da shi, yayin da aka shafe shekaru ana zargin maguɗi a dukkan zaɓukan kasar nan.
