
Masu zanga-zangar na neman a sako jagoran ’yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu ne a Abuja. Yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da harsasai masu rai domin tarwatsa su, a cewar rahotanni.
Lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin kan titunan Babban Birnin Tarayya inda masu zanga-zangar suka fito kusa da Fadar Shugaban Ƙasa, duk da umarnin kotu da ta haramta musu yin hakan.
Zanga-zangar ta samu jagorancin dan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar (AAC), Omoyele Sowore.
Shaidun gani da ido sun ce , masu zanga-zangar sun fara taruwa tun misalin karfe 6:50 na safe a kusa da ofishin Ma’aikatar Kula Harkokin Mata na Kasa.
Jami’an tsaron haɗin gwiwar ’yan sanda, da sojoji da DSS da na Sibil Difens (NSCDC) sun yi musu dirar mikiya bayan da Sowore da sauran ‘yan zanga-zangar suka fara rera wakokin neman a saki Nnamdi Kanu.
A daidai lokacin da suke ƙoƙarin wucewa kusa da Kotun Ɗaukaka Kara Ta kasa ne jami’an tsaro suka fara buɗe wuta. in ji majiyarmu.
Da farko masu zanga-zangar sun ɗauka harbin barkonon tsohuwa ne, mai sa hawaye, amma daga bisani aka tabbatar cewa harsasai na gaske ne ke tashi daga wurare daban-daban. In ji rahotanni.