Ministan Tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar ya sauka a kasar Mali
Ministan na ziyara ƙasar ce domin halartar baje-koli na ƙasa da ƙasa kan makaman tsaro.
Ya kuma sauka a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Modibo Keita da ke a babban birnin kasar Bamako a ranar Alhamis don soma ziyarar.
Badaru Abubakar ya samu tarbar takwaransa na Mali Janar Sadio Kamara.
Ana taron baje jkolin ne yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da fama da ƙalubalen tsaro sakamakon hare-haren ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
