Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana shirinta na fara cin tarar hukumomi da kuma kamfanoni da masu zaman kansu da aka samu da sakaci a fannin tsaftar muhalli.
Shugaban Kwamitin Tsaftar Muhalli na Jihar, kuma Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Muhalli, Abdullahi Abba Jahun, ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da kwamitin ya kai kananan hukumomin Babura da kuma Garki.
A cewarsa, ziyarar na da nufin duba yadda ake aiwatar da aikin tsaftar muhalli na ƙarshen wata, da kuma zaburar da shugabanni da kuma masu ruwa da tsaki kan mahimmacin aikin tsaftar muhalli.
- Gwamnatin Jigawa ta sanya hannu da wasu kungoyiyin lafiya kan magance matsalar gani
- Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da rabon kayan noma na Naira biliyan 1.5
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na da niyyar inganta muhalli don kare lafiyar al’umma, tare da kira ga kungiyoyi da kuma matasa da su ba da hadin kai domin samun nasarar shirin.
A nasu jawaban, shugabannin Kananan Hukumomin Babura da kuma Garki, Alhaji Hamisu Muhammad Garu da kuma Alhaji Adamu Hudu Kore, sun bayyana cewa wannan ziyarar ta ƙara musu kwarin gwiwa wajen ɗorewa tare da inganta tsaftar muhalli a yankunansu.
