Wasu Farfesoshi a Najeriya sun bukaci a daga albashinsu zuwa aƙalla naira miliyan biyu da rabi a wata, inda suka bayyana cewa duk abin da ya gaza haka bai dace ba.
tun a ranar Talata data gabata ne malama jami’oi suka gudanar da zanga-zanga a wasu jami’oin Najeriya inda mambobin ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU suka zargi Gwamnatin Tarayya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka sake nazari a shekarar 2009.
Malaman sun dade suna kuka kan ƙarancin albashi da kuma tabarbarewar yanayin aiki a jami’o’i.
A halin yanzu, Farfesa na samun kusan naira dubu 500 kacal a wata, abin da ya tilasta wasu rayuwa cikin ƙuncin matsuguni, har ma wasu suna fafatawa da ɗalibai wajen samun wurin hawa motar makaranta.
A wata hira da aka yi da jaridar Saturday Punch, wasu farfesoshi irin su Remi Aiyede daga Jami’ar Ibadan sun bayyana cewa malamai a Najeriya na samun albashi mai rauni idan aka kwatanta da abokan aikinsu a wasu ƙasashen Afirka, kuma akwai rahoton gwamnati da ya riga ya bada shawarar ƙarin albashi makamancin haka.
A Jami’ar Legas, Farfesa Abigail Ndizika-Ogwezzy ta ce dole a bai wa malamai albashi mai kyau domin su rika gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, yayin da Farfesa Sheriffdeen Tela na Jami’ar Babcock ya bayyana cewa banbancin albashin malaman jami’a da na manyan ’yan siyasa ba ya da hujjar karewa.
Shi ma tsohon shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce ya dace farfesoshi su rika samun albashi tsakanin naira miliyan daya zuwa miliyan biyar a wata.
