Ga wasu manyan abubuwa da suka ja hankalin jama’a a jihar Kano da ba za a manta da su ba a shekarar 2024 da muke bankwana da ita.
Tabbatar wa Gwamnan jihar Kano kujerarsa
A ranar 12 ga watan Janairu Kotu Kolin Najeriya ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf kujerarsa ta gwamnan Kano karkashin jam’iyyar NNPP. Bayan shigar da kara dake kalubalantar nasararsa da Nasiru Yusuf Gawuna da jam’iyyar APC suka yi.
Da farko Kotun sauraron korafe-korafen zabe ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben haka ita ma Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun baya.
Amma a Kotun Koli hukuncin ya sauya a inda Abba Kabir ya tabbata gwamnan Kano.
Ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi
Gwamman Kano ya ayyana dokar ta-baci ne a kokarinsa na ganin kowanne yaro ya samu ilimin faramare kyauta. Hakan ta sa gwamnati ta ware kaso 24 a cikin 100 ga harkar ilimi tare da mayar da malaman Hukumar Ilimin bai-daya SUBEB 3,366 bakin aiki da kuma daukar malaman BESDA 5,632.
Sannan gwamman ya dawo da gyaran makarantun firamare da kuma samar da kujerun zama ga dalibai da kuma dalibai
Gwamna Abba ya kuma dawo da dauka nauyin karatun dalibai zuwa kasashen waje don karo ilimi.
Da kuma fafado da makarantun koyon sana’oi guda 28 da gwamnatin baya ta dakatar da ayyukan su.
Saukar Shugaban Hisbah kan danbarwar ’yar Tiktok
A ranar Juma’a, 1 ga watan Maris, Sheikh Aminu Daurawa, Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ya yi murabus daga mukaminsa bayan sukar salon aikinsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Sheikh Daurawa ya bayyana murabus din ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook, yayin gudanar da wani taro tare da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano a garin Kaduna.
Ya kuma dauki wannan mataki ne a cewarsa bayan duk iya kokarinsa na kawo gyara musamman ga abin da ‘yan Tik tok suke yi da kuma’yan fim amma hakan da alama bai yiwa gwamnatin dadi ba.
Hakan sai ya yi daidai da lokacin da ake tsaka da cece-kuce kan Murja Kunya, wata ‘yar Tik-tok wacce aka alakanta da gwamnan.
Sheikh Daurawa ya koma bakin aikinsa a matsayin Shugaban Hisbah, bayan shiga tsakani da kuma ban baki da wasu dattawan jihar su ka yi.
Rushe masarautun Kano da sake dawo da Muhammadu Sunusi na II
Rushewar masarautun Kano ta hanyar dokar “Kano Emirates Council (Repeal) Bill 2024” da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu, ta cire Sarki Aminu Ado Bayero, ta kuma yi awon gaba da sauran sarakuna hudu da tsohon gwamnantin Ganduje ya nada.
Hakan ta mayar da sarkin Kano na 15 Muhammadu Sanusi II, kan karaga, kuma ya jagoranci sallar Jumu’a a fadar gwamnati jim kaɗan bayan karbar takardar nadinsa a hukumance.
Aminu Ado Bayero ya tare a gidan sarki na Nasarawa, a inda ya ci gaba da gudanar da mulkinsa na sarauta.
Daga bisani, shari’a ta biyo baya, inda kotuna suka yi ta bayar da umarnin da ke karo da juna wajen tabbatar da matsayin sarautar sarakunan biyu.
Kone masallata suna tsaka da salla
A ranar 15 ga Mayu 2024, wani mutum mai suna Shafi’u Abubakar, mai shekara 38, ya kona mutane 23 da suka taru don sallar asuba a wani masallaci a kauyen Abasawa dake karamar Hukumar Gezawa.
Wannan mummunan al’amari ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 23 da suka taru domin yin sallar asuba, inda wutar ƙone su har lahira tare da jikkata wasu kadan masu nisan kwana.
An gurfanar da wanda ake zargi a gaban Babbar Kotun Shari’a bisa tuhumar kisan kai da gangan, yunƙurin kisan kai da haddasa munanan raunuka da kuma haddasa barna ta hanyar kunna wuta.
Zanga-zangar yunwa
Zanga-zangar yunwa da aka gudanar a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tashin hankali inda mutane uku suka rasa rayukansu bayan lalata wasu shaguna da barnata wasu gine-ginen gwamnati.
Gwamna Kano ya sanya dokar ta-baci na sa’o’i 24 a jihar, yayin da aka kama mutane 269 bisa zargin tada hankalin jama’a.
A kuma rana ta biyar ta zanga-zangar, wasu masu matasan suka cigaba da zanga-zangar dauke da tutocin ƙasar Rasha a titin zuwa Zariya da titin gidan Zu, da titin Hadejiya da sauran wasu wurare.
‘Yan sanda sun kama wasu daga cikinsu an kuma wuce da su zuwa Abuja.
Dambarwar Kwangilar magunguna
Rikici ya barke kan wata yarjejeniyar magunguna ta Naira miliyan 440 da ta shafi kananan hukumomi 44 na jihar.
PCACC ta kaddamar da bincike kan zargin damfara a kwangilar samar da magunguna wanda aka kiyasta kudinsa ya kai Naira miliyan 440. Hukumar ta gano wata matsala a kwangilar gyaran rijiyoyin burtsatse, wanda aka ƙiyasta kuɗinsa ya kai kusan Naira miliyan 660.
Binciken ya kai ga tuhumar wasu jami’ai, ciki har da Sakatare Dindindin na Ma’aikatar Harkokin ƙananan Hukumomi da Masarautu, Mohammed Kabara da Shugaban reshen jihar na ƙungiyar ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON), Abdullahi Ibrahim Bashir da wasu jami’ai na Ma’aikatar ƙananan Hukumomi, waɗanda aka fara tsarewa.
Hatsaniyar kwamishiniya da likita
Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA) ta dakatar da ayyuka a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad bayan wani rikici tsakanin Kwamishiniyar Jin ƙai da wata likita.
Kakakin Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA), Dakta Muhammad Aminu Musa, ya ce binciken da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar ya tabbatar da cewa likitar ba ta yi kuskure ba a lamarin, inda aka tabbatar da cewa ta yi aiki cikin cikakkiyar ƙwarewa.
Wannan ya jawo cece-kuce har sai Gwamna Yusuf ya shiga tsakani kuma aka warware matsalar.
Sauke Sakataren Gwamnati da wasu kwamishinoni
A ranar 14 ga Oktoba Jam’iyyar NNPP ta Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnati Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri Muhammad Diggol saboda zargin rashin ɗa’a da goyon bayan wata ƙungiya mai suna “Abba Tsaya da ƙafarka” wacce ake ganin tana neman ruguza tasirin Kwankwasiyya.
Har ila yau, wasu ‘yan majalisar NNPP biyu, Aliyu Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum, an zarge su da ingiza rikicin, bayan da suka fito fili suka nuna goyon bayansu ga NNPP ƙarƙashin jagorancin Chief Boniface Aniebonam, wacce ta yanke alaƙa da tafiyar Kwankwasiyya.
Mayar da sunan Jami’ar Northwest sunanta na asali
Jam’iar Yusfu Maitama Sule ta koma Jam’ir Nortwest na asali a wani zama da majalisar zartarwata jihar ta yi a watan a Nuwamba.
Sannan ta kuma sa wa Makarantar Share Fagen shiga jami’a dake Tudun Wada suna na Maitama Sule.
Ranar 30 ga watan Disamba kuma Majalisar Dokoki ta jihar ta amince da wannan sauyin suna.