Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe daukacin makarantun firemare da na sakandiri da kuma masu zaman kan su saboda dalilan tsaro.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi na jihar Bauchi Jalaludden Usman ya fitar a ranar Litinin.
“An dauki matakin ne biyo bayan shawarwarin da dama bisa la’akari da yanayin tsaro a jihar ta Bauchi”. In ji sanarwar
Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da malamai da masu makarantun da su kwantar da hankalinsu tare da mara wa gwamnatin jihar baya domin kare rayukan ɗaliban.
Gwamnatin jihar ta kuma ce tana aiki tare da hukumomin tsaro domin magance matsalolin cikin gaggawa tare da tabbatar da komawar makarantu kan tsarin da zarar an samu kwanciyar hankali.
