Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce kasar Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutane aƙalla 347 a shekarar 2025, alƙaluman da suka zarce na shekarar 2024.
A cewar wani rahoto da gamayyar ƙungiyoyin suka fitar a karshen mako.
“Mafi yawan waɗanda aka zartar wa hukuncin kisan a Saudiyya masu safarar miyagun ƙwayoyi ne, kuma fiye da rabin su ƴan ƙasashen waje ne” In ji rahoton.
Fursunonin baya bayan nan da aka zartar wa hukuncin kisa ƴan asalin ƙasar Pakistan ne masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Akwai kuma wani ɗan jarida da wasu matasa da suka aikata laifi tun suna ƙananan yara da kuma wasu mata biyar.
