
Asusun tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya yi gargaɗin cewa yunwa na barazana ga rayukan yara sama da dubu 420,000 daga cikin miliyan 3 da dubu 500 da ke cikin tsananin buƙatar abinci mai gina jiki a kasar nan.
Jami’ar da ke kula da shirin UNICEF a kasar nan, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatef ce ta yi gargaɗin yayin ziyarar da ta kai a Maidurin a jihar Borno a jiya alhamis.
Wafaa Elfadil ta ce Najeriya na da yara aƙalla miliyan 15 dake fuskantar matsalar ƙarancin abinci, yayin da miliyan 3 da dubu 500 daga cikinsu ke tsananin buƙatar abinci mai gina jiki, a don haka yara dubu 420,000 na iya mutuwa saboda yunwar a shekarar 2025 idan har ba’a ɗauki matakin gaggawa ba.
Wafaa Elfadil ta ce idan har ba’a yi amfani da kuɗaɗe wajen yin abinda ya da ce ba, to tabbas Najeriya na cikin barazanar rasa dubbun yara sanadiyyar ƙarancin abinci da cutuka da kuma rashin kulawar da ta dace.
ta kuma yi bayani kan yadda a halin yanzu UNICEF ke buƙatar ƙarin kuɗaɗe cikin gaggawa, da ƙara faɗaɗa cibiyoyin kula da lafiyarta domin tabbatar da cewa babu yaron da rasa ransa sanadiyyar yunwa a ƙasar.
Ta ƙara da cewa yankin Arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da zama wanda yafi fuskantar matsalar agaji, inda sama da mutane miliyan 4 da dubu 500 ke tsananin buƙatar tallafi.