Jam’iyyar PDP ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki SAN, a matsayin sabon shugabanta.
Turaki ya hau matsayin ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Ibadan babban birnin Oyo.
Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar hawa mukamin ne bayan da doke Sanata Lado Ɗan Marke da yawan ƙuri’un da aka kada a yayin taron.
BBC ta rawaito sabon shugaban ya samu kuri’u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar daga jimlara wakilai 3, 131 suka halarta.
A kujeru biyu ne aka yi zaɓe akan su, yayin da dama daga sauran kujerun shugabancin jam’iyyar aka yi maslaha a tsakanin ƴan takara.
Daga bisani aka kira wakilai daga jihohi suka kaɗa ƙuri’unsu kamar yadda dokar hukumar zaben Najeriya ta tanada.
An zabi sabbin shugabannin jam’iyyar da za su ja ragamarta har zuwa shekaru hudu masu zuwa.
